An naɗa farfesa mafi ƙarancin shekaru a matsayin shugabar Jami’ar Abuja

Spread the love

An nada Farfesa Aisha Sani Maikudi a matsayin shugabar jami’ar Abuja bayan cikar wa’adin mulkin shugaban jami’ar na shida, Farfesa Abdulrasheed Na’Allah.

Hukumar gudanarwar jami’ar ce ta naɗa ta kan wannan muƙamin a matsayin riƙo zuwa lokacin da za a ƙaddamar da majalisar jami’ar da kuma naɗa cikakken shugaban jami’ar.

Farfesa Maikudi, ƙwararriya ce a fannin ilimin shari’a ta duniya kuma ita ce mataimakiyar shugaban jami’ar mai kula da ɓangaren koyo da koyarwa.

An haifi farfesa Aisha Sani Maikudi, yar asalin jihar Katsina, a birnin Zaria da ke jihar Kaduna ranar 31 ga watan Janairun 1983.

Farfesar Maikuɗi ita ce farfesa mafi ƙanƙantar shekaru a jami’ar Abuja.

Ta samu shaidar kammala makarantar sakandare a Queens College da ke Legas. Bayan nan kuma, ta yi digiri na farko da na biyu a jami’ar Reading da London School of Economics a Burtaniya kan ilimin shari’a.

Ta kuma je makarantar horas da lauyoyi ta Najeriya da ke Abuja daga nan kuma ta yi digirinta na uku a jami’ar Abuja duk a fannin na shari’a.

Farfesa Aisha ta yi wa kasa hidima karkashin shirin NYSC a shekarar 2007. Sannan ta soma koyarwa a jami’ar Abuja a 2008, ta kuma zama mace ta farko kuma mafi karancin shekaru da ta shugabanci sashen koyar da ilimin shari’a a 2014, kuma mace ta farko mafi karancin shekaru da ta zama mataimakiyar shugaban sashen a 2018. Ta kuma kafa tarihin zama darakta ta farko a jami’ar ta Abuja.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *