An naɗa Tuchel a matsayin sabon kocin Ingila

Spread the love

An naɗa Thomas Tuchel a matsayin sabon kocin Ingila. Kwantiragin zai fara ne daga 1 ga watan Janairun 2025.

Ɗan ƙasar Jamus mai shekara 51, ya zama mutum na uku da zai jagoranci Ingila wanda ba ɗan ƙasar ba, bayan Sven-Goran Eriksson da Fabio Capello.

Gareth Southgate ya yi murabus a watan Yuli bayan shan kashi da Ingila ta yi a hannun Sifaniya a wasan karshe na Gasar Euro 2024.

Lee Carsley, wanda aka naɗa a matsayin kocin riƙon kwarya a watan Agusta, zai ci gaba da riko a wasannin Gasar Nations League da Ingila za ta yi da ƙasashen Greece da kuma Jamhuriyar Ireland a wata mai zuwa.

Tuchel, wanda ya bar Bayern Munich a karshen kakar wasanni da ta gabata, ya ce: “Ina alfahari da wannan dama da aka ba ni na jagorantar tawagra Ingila.

“Na daɗe da son irin salon wasa da ake yi a ƙasar nan, kuma tuni na fara jin daɗin matsayi da na samu,” in ji Tuchel.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *