Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince da naɗin sabbin shugabannin ƙungiyar ƙwallon kafa ta Kano, Pillars.
Pillars, wadda ake kira ”sai masu gida” ba ta da shugabanni tun bayan da aka kori Babangida Little daga jagoranci.
A wata sanarwa da aka fitar daga ofishin kwamishinan matasa da wasanni, Mustapha Rabiu Kwankwaso ta sanar da mutum 14 da za su ja ragamar Pillars.
Ali Na Yara mai Samba shi ne sabon shugaba a matakin rikon kwarya na shekara ɗaya tare da Abubakar Isa Dandago a matakin jami’in yaɗa labaran ƙungiyar.
Kano Pillars, wadda ta kare a mataki na 11 a gasar Premier League ta Najeriya da ta wuce, na fatan taka rawar gani a kakar 2024/25.
Za a fara gasar Premier ta Najeriya daga 31 ga watan Agusta, inda aka tanadi naira miliyan 200 ga duk wadda ta lashe kofin bana.
Jerin shugabannin Kano Pillars
1. Aliyu Nayara Mai Samba – Shugaba
2. Salisu Muhammad Kosawa – Mamba
3. Abubakar Isa Dandago – Jami’in yaɗa labarai
4. Ismail Abba Tangalash- Mataimakin Jami’in yaɗa labarai
5. Yusuf Danladi Andy Cole – Mamba
6. Muhammad Usman – Mamba
7. Ahmad Musbahu – Mamba
8. Umar Umar Dankura – Mamba
9. Rabiu Abdullahi – Mamba
10. Nasiru Bello- Mamba
11. Muhammad Danjuma Gwarzo – Mamba
12. Mustapha Usman Darma – Mamba
13. Muhammad Ibrahim (Hassan West) – mamba
14. Engr Usman K/Naisa- Mamba