An naɗa Saifullahi Muhammed a matsayin Kwamandan Hukumar Tsaron Dajin Najeriya shiyyar Arewa maso Yamma

Spread the love

 

Hukumar Tsaron Dajin Najeriya (NFSS) ta nada Saifullahi Muhammed, dan asalin karamar hukumar Birni a jihar Kano, a matsayin kwamandan shiyyar Arewa maso Yamma, Wannan nadin ya zo ne bisa jajircewarsa da ƙoƙarin sa wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya a Najeriya.

Nadin wanda ya fara aiki daga ranar 13 ga watan Janairun 2025, ya samu amincewa tare da sanya hannun babban kwamandan Hukumar Tsaron Dajin Najeriya, Amb. Osatimeh Joshua, da Shugaban Kwamitin Amintattu, AIG (Rtd) E. E. Amakulor, kamar yadda yake a doka ta 5, 6, karamin sashe na A da B na kundin tsarin mulkin Majalisar Hukumar Tsaron Dajin Najeriya.

A jawabinsa na karbar aiki, Saifullahi Muhammed, ya bayyana jin dadinsa bisa amincewar da shugabancin hukumar NFSS ta yi masa. Ya jaddada kudirin sa na ci gaba da inganta ayyukan hukumar a shiyyar Arewa maso Yamma.

 

“Abin alfahari ne gare ni da aka danƙa min wannan nauyi. Zan himmatu wajen inganta ayyukan Hukumar Tsaron Dajin Najeriya a shiyyar Arewa maso Yamma, kuma zan yi aiki ba tare da gajiyawa ba da duk masu ruwa da tsaki don tabbatar da cewa Najeriya ta zama wuri mafi aminci da zaman lafiya ga kowa da kowa.”

 

Da wannan nadin, Saifullahi Muhammed zai zama cikin sahun shugabanni masu hangen nesa da aka dorawa alhakin karfafa ayyukan tsaro a fadin Najeriya. Zai kuma inganta hadin gwiwa da al’ummomin yankin, hukumomin tsaro, da sauran masu ruwa da tsaki don kawo ƙarshen matsalolin tsaro a yankin.

Hukumar Tsaron Dajin Najeriya ta sake jaddada kudirinta na bada karfin gwiwa, karfafa tsaro da kuma bayar da gudumawa wajen samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a ƙasar nan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *