Dan majalissar dokokin jihar Kano mai wakiltar al’ummar karamar hukumar Rano, RT Hon. Ibrahim Malami Rano, ya nada Naziru Salihu Rano ( Dagzee Salihu Rano) a matsayin babban mai taimaka masa na musamman kan kafofin yada labarai.
Takaddar nadin Mai kwanan watan 11 ga watan maris 2025, Mai dauke da sa Hannun Dan majalissar dokokin Hon. Ibrahim Malami Rano.
Dan majalissar ya taya Dagzee Salihu Rano, murna tare da yi masa fatan Alkairi.
Dagzee ,ya bayyana godiyarsa ga Allah madaukacin sarki, bisa wannan mukami da ya samu, Inda ya Yi alkawarin jajircewa don ya tabbatar da ya sauke nauyin da aka Dora masa