Hukumar gudanarwar gidan Rediyon Tech FM dake jihar Kano ta amince da nada Suyudi Isah Jibril Bichi , a matsayin sabon shugaban tashar.
Nadin nasa na cikin wata takardar da aka fitar mai kwanan watan 13 ga Oktoba 2025, wacce Manajan Darakta na kamfanin, Mukhtar Tajuddeen Usman, ya sanya wa hannu tare da cewa nadin ya fara aiki nan take.
Suyudi Isah Jibril Bichi yana da Dibloma da digiri na farko (BSc) a fannin aikin Jarida, kuma yanzu haka yana ci gaba da karatun digiri na biyu (Masters) a fannin hulda da jama’a (Public Relations) a Jami’ar Bayero Kano (BUK)
- An Kama Yan Sadan Bogi 5 Da Zargin Cutar Da Mutane A Kano.
- Mai Neman Tsayawa Takarar Majalissar Wakilai A Wudil/Garko Barista Ahmad S. Bawa Ya Bukaci Yan Nijeriya Su Yi Rijistar Zabe Don Kada Gwamnatin Tinubu A 2027
Suyudi Bichi na da ƙwarewa mai zurfi a harkar yada labarai da aikin jarida, wanda ya samu gogewa ta tsawon shekaru sakamakon aiki da ya yi a kafafen yada labarai daban-daban.
Kafin wannan mukami, Suyudi Bichi ya rike matsayin shugaban tashar Guarantee Radio, tsawon shekaru biyu.