An rantsar da Ododo a matsayin sabon gwamnan Kogi

Spread the love

Usman Ododo ya sha rantsuwar kama aiki a matsayin sabon gwamnan jihar Kogi da ke tsakiyar Najeriya, bayan nasarar lashe zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar cikin watan Nuwamba.

An gudanar da bikin rantsuwar ne a Lokoja babban birnin jihar ranar Asabar da rana, inda aka rantsar da shi tare da mataimakinsa, Salifu Joel Oyibo.

Ana zanga-zanga kan yawan kashe mata a Kenya

Mista Ododo wanda ɗan jam’iyyar APC ne zai maye gurbin Yahaya Bello wanda ke kammala wa’adin mulkinsa na biyu.

Mataimakin shugaban Najeriya Kashim Shettima, da gwamnan jihar Yahaya Bello da wasu jiga-jigan jam’iyyar APC, na daga cikin mutanen da suka halarci bikin rantsuwar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *