An rufe kantin China kan zargin nuna wa ƴan Najeriya wariya

Spread the love

Jami’an hukumar kare haƙƙin masu sayen kayayyaki FCCPC a Najeriya ta garƙame wani kantin sayar da kayayyaki na ƴan China da ke Abuja, babban birnin ƙasar.

Jami’an hukumar ta FCCPC sun rufe kantin ne bayan da suka yi dirar mikiya a wajen ranar Litinin saboda zargin yadda ake nuna wa ƴan Najeriya ƙyama.

Jami’an hukumar sun ɗauki matakin ne bayan da suka yi wa ma’aikatan wurin ƴan Najeriya tambayoyi.

Tun farko, a ranar Lahadi ne al’umma suka bayyana damuwa game da yadda ake hana ƴan Najeriya shiga kantin na China.

Jami’in da ke kula da kantin, Shaibu Sanusi ya tabbatar cewa ƴan Najeriyar da ke aiki a wajen ne kaɗai suke iya zuwa yin siyayya ban da sauran ƴan Najeriya.

Hukumar ta ɗauki matakin ne bayan da jama’a a shafukan sada zumunta suka yi ta cece-kuce game da yadda aka ce kantin ke hana ƴan Najeriya zuwa siyayya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *