An rufe yaƙin neman zaɓe a Chadi

Spread the love

An rufe gangamin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da ake yi a Chadi, kwana guda gabanin fara babban zaɓen ƙasar.

Za a gudanar da zaɓen ne a gobe Litinin, wata rana da aka dade ana jira domin mayar da ƙasar kan turbar dimokradiyya.

Kimanin makonni uku kenan da ‘yan takarar shugaban ƙasar su 10 ke ta yawon neman zaɓe a fadin kasar, domin shaidawa magoya bayan shirinsu na ciyar da ƙasar gaba ta fuskar rayuwa da siyasa da kuma tattalin arziki.

Da yake rufe nasa yaƙin neman zaɓen a N’Djamena, jagorar mayar da ƙasar ga gwamnatin farar hula Mahamt Deby ya shaida wa magoya baya da jam’iyyun kawance cewa akwai kwarin gwiwa kan sakamakon zaɓen.

“Zan iya cewa akwai gamsuwar nasararmu a ranar 6 ga watan Mayu tabbatacciya ce,” in ji Janar Mahamat Deby.

Ya kuma jaddada sabonta ƙawancensu da ƙasashen da mutunta Chadi a matsayin ƙasa mai cikakken ‘yanci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *