An yi garkuwa da wani mutum mai shekara 79 a duniya, Kwamared Elder Takai Agang Shamang a gidansa da ke Bikini-Tsourarang, Manchock a ƙaramar hukumar Kaura ta Jihar Kaduna.
Aminiya ta ruwaito cewar an sace shi ne da misalin ƙarfe 7:30 zuwa ƙarfe 8 na daren ranar Juma’a.
Misis Grace Yohannah Abbin, wadda ’ya ce ga mutumin, ta tabbatar da faruwar lamarin da safiyar Lahadi.
A cewarta, wasu gungun mahara sun kutsa cikin gidan mahaifinta da ƙarfi kuma suka tafi da shi.
Kwamared Shamang, ya yi fice wajen gudanar da ayyukan jin-ƙai da ƙungiyar ƙwadago kuma mutum ne wanda ake girmamawa a yankin.
- Kotu ta umarci Sadiya Farouk ta faɗi yadda aka kashe naira biliyan 729 don raba wa talakawan Najeriya tallafi a 2021
- Wani Da Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Ya Shaidawa Yan Sanda Cewa, Tsoron Kar Ya Mutu Ne Ya Sanya Shi Tserewa Daga Dajin Zamfara Zuwa Kano.
Ta ce hukumomi a Jihar Kaduna na gudanar da bincike kan lamarin.
“Al’umma da ’yan uwa suna kira ga jama’a su taimaka da duk wani bayani da zai taimaka wajen dawowarsa lafiya,” in ji ta.
Kakakin rundunar ’yan sandan Kaduna, Mansir Hassan, bai ce komai game da faruwar lamarin ba zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.