Wasu Gungun yan bindiga sun kai hari, a Sabuwar Unguwa dake jihar Katsina, tare yin garkuwa da wasu ma’aurata da kuma yarsu mai suna Jidda Anas, sannan suka halaka wani jami’in bijilanti.
Rahotanni na cewa yan bindigar sun shiga cikin unguwar da misalin karfe 3:00am na daren ranar talata, inda suka shiga gidan, Anas Ahmadu da matarsa Halimatu wadda take dauke da juna biyu da kuma yarsu Jidda mai shekaru 2.
- Yan Sanda Za Su Binciki Wasu Yan Karota Kan Batan Kudin Wani Lauya A Cikin Motar Da Suka Dauka
- Yan Sanda Za Su Binciki Wasu Yan Karota Kan Batan Kudin Wani Lauya A Cikin Motar Da Suka Dauka
Jami’in bijilantin mai suna Abdullahi Muhammad, ya rasa ransa ne lokacin da yake kokarin bayar da taimako ga ma’auratan da aka yi garkuwar da su.
Rundunar yan sandan jihar Katsina, ta bakin mai magana da yawun ta, DSP Abubakar Sadiq Aliyu, ya tabbatar da cewa sun fara gudanar da bincike kan faruwar lamarin.