Ana zargin wasu matasa 2 da laifin sace wata wayar salula wacce kimar kudinta ya haura naira dubu dari 2
Al’amarin ya Faru ne a ranar Lahdi da misalin karfe 11:40 na dare lokacin da Ake zargin matasan Yan asalin unguwar Kurna Layin gidan Kara a jahar Kano , wadanda suka je Kurna Tudun Bojuwa don aikata sata.
An kama su a kantin Umar Dan fari suna kikkifta idanun ungulu taga abincinta a shadda gidan turoso, bayan sun dauke wayar wani a Dattijo a cikin Aljihunsa.
Matasan sun buge da siyan alawar madara ta naira dari kachal, sannan suna ta musayar sigina da girar idanu don yin harkalla, basu nemi barin kantin ba sai da suka tabbatar sun raba Dattijon da wayar sa, wanda daga bisani dubu dayan su ta cika aka haushi jibgarsa.
Injiniya Auwalu Ahmad dan Dattijon da aka daukewa wayar da kuma Umar Isah Usman Mai kantin da suke je siyan alawar madarar , sun yi kira matasa da su Nemi na kansu.
- An Tura Kwararrun Yan Sanda Don Kubutar Da Daliban Da Aka Sace A Benue
- Ɗan wake ya yi ajalin uwa da ’ya’yanta 5 a KanoShima matashin da aka yi ram dashi kan zargin hada baki da sace wayar sama da naira dubu 2 Mai suna Muhammad Aliyu, ya ce tasautsayi ne kuma ba zai sake yi ba , domin wannan ne karon farko da abokin na sa ya kirawo shi har suka aikata laifin.
- Saurari muryar Wanda Ake Zargin
-
Tuni dai wasu jajirtattu mutane a yankin suka danka shi a hannun jami’an ‘yan sanda na Diragon dake Kurna Babban Layi Filin Shinge bayan sunyi uwa da makarbiya wajen hana fusatattun matasan yankin daukar doka a hannun su.