An sake kama fursunoni 51 da suka tsere daga gidan yarin Maiduguri

Spread the love

Hukumar gidan gyaran hali ta Najeriya ta ce ta sake kama wasu fursononi cikin waɗanda suka tsere daga gidan yari a Maiduguri na jihar Borno lokacin ambaliyar ruwan da aka yi a watan Satumba da ya gabata.

Kakakin hukumar, Abubakar Umar ya shaida wa BBC cewa an samu nasarar sake kama 51 daga cikin mutanen 271 da suka tsere.

Ya kuma ce suna aiki haɗin gwiwa tsakaninsu da jami’an tsaro da dama, inda ya ce suna bai wa juna bayanan sirri da zai taimaka musu wajen yin aiki.

“Lokacin da abin ya faru, fursunoni 271 ne suka tsere. Yanzu mun yi nasarar sake kama 51 daga cikinsu,” in ji Umar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *