An sallami sojar da ta zargi shugabanta da neman lalata da ita

Spread the love

Rundunar Sojin Ƙasan Najeriya ta sallami wata ƙurtu sojan da ta zargi wani babban soja da yunƙurin yin lalata da ita.

Rundunar ta ce ta sallami ƙaramar dokar mai muƙamin Private daga aiki ne bayan ta kammala bincike kan zargin da ta yi.

Kakakin rundunar, Onyema Nwachukwu, ya bayyana cewa bayan kammala zuzzurfan binciken da aka gudanar, an gano cewa babu ƙamshin gaskiya a zargin da Private Ruth Ogunyele ta yi wa Kanar I.B Abdulkareem.

Onyema Nwachukwu ya cewa,  hasali ma binciken ya gano cewa Private Ruth Ogunyele ta samu taɓin ƙwaƙwalwa.

A sakamakon haka ne rundunar ta yanke shawarar sawwaka mata daga aikin soji.

Amma ya ce duk da sallamar ta daga aiki da aka yi, za a biya ta kudaden garatuti kuma za ta rika karɓar fansho.

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *