Akalla mutane 38 ne suka rasa rayukansu sakamakon tashin gobara a watanni shidan farkon shekarar 2025.
Kakakin hukumar kashe gobara na jihar Kano, ACFO Saminu Yusuf Abdullahi, ne ya bayyana hakan lokacin da yake yin karinhaske.
Ya ce daga ranar 1 ga watan Janairu zuwa Yunin 2025, sun sami kiran tashin gobara guda 402 a wurare dabam-daban dake fadin jihar.
Saminu Yusif, ya kara da cewa sun samu kiraye-kirayen karya guda 46, sai kiran neman agajin gaggawa guda 63, an kuma rasa rayukan mutane 38.
Hukumar ta ce yawancin mutanen sun rasu ne sakamakon fadawa ruwa da tashin gobara ko kuma hatsarin kan hanya.
- Jami’an sa-kan Zamfara sun kashe Kacalla Ɗanbokolo ubangidan Turji
- Cikin Hotuna : Yadda Kwamitin PCRC Na Area Command Eastern Bypass Kano Ya Rantsar Da Sabbin Shugabanni
Haka zalika hukumar ta ce ta samu nasarar ceto rayukan mutane 48 tun daga farkon shekarar zuwa yanzu.
An samu salwantar dukiya sanadiyar tashin gobara ta naira biliyan daya da miliyan goma sha daya da dubu dari bakwai da talatin da naira goma.
Hukumar ta kuma tseratar da dukiya daga iftila’in gobara data kai naira biliyan goma sha biyu da miliyan dari bakwai da saba’in da tara da dubu dari hudu da arba’in da tara da dari da tara.
A karshe ya yi kira ga al’umma kan yadda suke mu’amula da wuta da Zarar sun kammala su dinga kashe wa.