An samu ƙaruwar gobara a Kano saboda shigowar hunturu

Spread the love

Hukumar kashe gobara a Kano ta ce an samu ƙarin tashin gobara a faɗin jihar sakamakon shigowar yanayin hunturu a wasu yankunan arewacin Najeriya.

Kakakin hukumar Saminu Yusuf Abdullahi ya shaida wa BBC cewa kafin zuwan yanayin hunturun an samu raguwar tashin gobara a jihar – wadda ita ce cibiyar kasuwancin arewacin ƙasar.

Saminu Yusuf Abdullahi ya ce a watan Nuwamban da ya gabata kaɗai an samu tashin gobara a jihar har sau 43, sakamakon yadda mutane ke ƙara ta’ammali da wuta a lokacin na hunturu.

”Adadin ya ninka, domin a watan Oktaba an samu matsalar tashin gobara a Kano sau 24, amma sakamakon shigowar hunturu a watan Nuwamban adadin ya kai 43”, in ji shi

Ya kuma ce daga shigowar watan Disamba, zuwa yanzu hukumarsu ta samu labarin tashin gobara har sau bakwai, zuwa yanzu.

Haka kuma hukumar kashe gobarar jihar ta ce mutum uku sun mutu, yayin da aka yi asarar dukiya da ta kai naira miliyan 130, a cikin watan da ya gabatan sakamakon tashin gobarar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *