An samu hatsaniya a majalisar dokokin jihar Zamfara bisa tabarbarewar tsaro

Spread the love

A Najeriya, yau wa su ‘yan majalisar dokokin jihar Zamfara sun harzuka, game da abin da suka kira ‘gazawar gwamnatin jihar wajen magance matsalar tsaro da ta addabi sassan jihar’.

Har ma sun ayyana rufe majalisar dokokin, sai al’amuran tsaro sun inganta a jihar.

Sai dai kuma wani bangare na ‘yan majalisar dokokin jihar ya musanta wannan batu, yana mai cewa gwamnan jihar yana yin iya bakin kokarinsa ta fuskar tsaron, kuma majalisar na nan bude.

Da alamu dai an fara zama irin na ’yan marina a majalisar dokokin jihar Zamfara, har wani bangare na ‘yan majalisar ya bayar da sanarwar rufe majalisar, harsai yadda hali yayi.

Babban hafsan sojin Najeriya ya gargaɗi masu neman a yi juyin mulki

Kotu Ta Umarci Ɗan Baba Impossible Ya Yi Rantsuwa Kan Zargin Dalla Wa Likita Mari

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *