Rundunar yan sandan jahar Kano, ta bayyana cewa ta samu karuwar korafe-korafen kisan kai da kuma ambaliyar ruwa da yake cinye mutane a fadin jahar.
Kakakin rundunar yan sandan jahar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanrwar da fitar a ranar Alhamis, a madadin kwamishinan yan sandan jahar CP Salman Dogo Garba.
Sanarwar ta ce rundunar ta yi duba na musamman akan korafe-korafen da ake samu na kisan kai , wanda daga fada sai a chakawa mutum wuka ko kuma tsintar gawar da ruwa ya cinye.
SP Abdullahi kiyawa , ya kara da cewa , wadannan abubuwa suna sanya al’umma cikin damuwa, wanda ya zamo dole a kara sanya ido kan yaya, yara , matasa don nusar da su kan matsaloli.
Cikin shawarwarin da rundura ta bayar sun hada da, a guji duk wani fada ko hada jiki don kaucewa abunda zai haifar da riciki da rigima, haka zalika a guji daukar wani makami da suka hada da Wuka, Gora, Fashasshiyar Kwalaba da kuuma karafa.
Saurari Muryar kakakin rundunar yan sandan Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa
Sannan a kula da wuraren da ake zama duk idan akaga wani makami a dauke shi, domin magance matsalar.
Rundunar ta shawarci matafiya musamman lokacin da ake ruwan sama , a guji shiga ruwa ko tsallake ruwan da ba a san zurfinsa ba.
Kwamishinan yan sandan jahar CP Salman Dogo Garba, ya bayar umarnin fadada bincike a wuraren da ake yawan samun korafe-korafen kisan kai .
A karshe rundunar ta yi kira ga jama’a, a duk lokacin da suka ga wani abu da ba su amince da shi, su gaggauta sanarwa a ofishin yan sanda mafi kusa don daukar matakin da ya dace ko kuma a kira nambar waya kamar haka 08032419754, 08123821575 da 09029292926