Karon Farko Yar Asalin Jihar Kano Ta Zama Kwamishiniyar Yan Sanda

Spread the love

 

A ranar Alhamis ne Hukumar kula da aiyukan Ƴan sanda, PSC ta ƙara wa Hauwa Ibrahim Jibrin girma zuwa muƙamin kwamishina (CP).

Hakan na zuwa ne a lokacin da aka ƙara wa manyan jami’ai 27 girma da suka haɗa da; kwamishinoni 11 da suka zama AIG, wato muƙamin mataimakin sufeton Yan Sandan Nigeria, da wasu 16 da suka zama kwamishinoni waɗanda tana ɗaya daga cikin su.

An haifi Hauwa Ibrahim ne a ranar 28 ga watan Oktoba, 1972 a ƙaramar hukumar Fagge ta jihar Kano.

Ta kuma yi karatun digiri a sashen Nazarin Siyasa da Difuloma a sashen Nazarin Tsaro da kuma digiri na biyu a ɓangaren.

A halin yanzu tana karatun digiri na uku. Kuma ita ce ƴar Arewa ta farko da ta samu muƙamin kwamishinar ƴan sanda.

Gabannin ƙara mata matsayin, ƴar sandan ta yi aiki a matsayin mukaddashiyar  kwamishinan ƴan sandan Abuja, sashen gudanarwa.

PSC, ƙarƙashin jagorancin Hashimu Argungu ta gudanar da rubutacciyar jarrabawa da kuma ta baka ga waɗanda aka ƙara wa muƙaman don tabbatar da gaskiya da adalci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *