
Rundunar yan sandan jihar Kano, ta bayyana cewa zata dauki tsattsauran mataki ga wadanda suke yada labaran karya ko jita-jitar fadan daba da kwacen waya, don firgita jama’a haka kawai ba tare da wani cikakken dalili ba.
Kakakin rundunar yan sandan jihar SP Abdullaahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da gidan Telebijin da radio na Muhasa, a ranar Litinin.
Wannan na zuwa ne yayin da ake samun wasu mutane da razana al’umma, a cikin unguwannin Kano duk da cewar an samu raguwar aikata aikata laifukan fadan daba da kuma kwacen wayar.
SP Abdullahi Kiyawa, ya ce daga 1 zuwa 7 gawatan Yunli 2025, an samu raguwar aikata laifukan, sakamakon hadin kan da al’umma suke bayarwa, kuma yawancin wadanda ake kama yan unguwannin da suka aikata laifin ne.
‘’idan matasa suka je unguwa suka yi satar waya abun mamaki sai kaga yan unguwar ne, ba wai abu ne mai dadi ba kaji ana kama yan unguwa da laifin fashin wayoyin mutane’’.
Ya kara da cewa duk wuraren da ake yin fadan daba ko kwacen waya, mutane sun fara yin kukan kura wajen kama wadanda ake zargi sannan su mika su hannun jami’an yan sanda.
Kiyawa, yaja hankalin masu yada jita-jitar fadan daba , da su daina idan ba a haka ba , za a kama su a gudanar da bincike kafin gurfanar da su a gaban kotu.
A karshe rundunar ta ce duk inda aka ji ana yada jita-jita, a yi kokarin sanarwa jami’an yan sanda ta hanyarsu kiransu a lambobin waya.