An samu raguwar kashe-kashe da garkuwa da mutane a Najeriya – Rahoto

Spread the love

Najeriya ta samu raguwa a yawan mutanen da ake kashewa, da waɗanda ake garkuwa da su, da kuma ayyukan rashin tsaro a cikin watan Yuni, idan aka kwatanta da watan Mayu na shekarar da muke ciki ta 2024.

Hakan na ƙunshe ne cikin rahoton wata-wata na al’amuran tsaro da kamfanin Beacon Consulting mai nazari kan harkokin tsaro ya fitar a yau Litinin.

Rahoton ya ce: “A watan Yunin 2024 an samu raguwar kai hare-hare, inda aka kai hari sau 618. Wannan na nuna cewa an samu raguwar kai hare-hare da kashi 19.32 cikin 100 idan aka haɗa da hare-hare 766 da aka kai a watan Mayu”.

Haka nan rahoton ya nuna cewa an samu raguwar matsalar garkuwa da mutane a Najeriyar cikin watan na Yuni da kimanin kashi 58.59 cikin 100.

A ɓangaren kashe-kashe kuwa, shi ma rahoton ya una cewa an samu raguwa da kashi 5.96 cikin 100.

“An kashe mutum 1,090 a watan Mayun 2024, inda a Yuni abin ya ragu zuwa 1,025 a watan Yuni.”

Harin ƙunar baƙin wake da ƙungiyar Boko Haram ta kai a garin Gwoza na jihar Borno, wanda ya kashe aƙalla mutum 30 a ƙarshen watan Yuni, ya ƙara fito da matsalar tsaro da ake fuskanta a sassa daban-daban na ƙasar.

Sai dai gwamnatin Najeriya ta sha yin iƙirarin tarwatsa ƙungiyar.

Haka nan, ƴan fashin daji na cigaba da kai samame suna kashe mutane da garkuwa da su a jihohi kamar Zamfara, da Katsina, da Kaduna, a arewa maso yammacin ƙasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *