An samu ƙaruwar satar mutane a Najeriya

Spread the love

Wani rahoto da kamfanin Beacon Consulting da ke nazarin tsaro a Afirka ta yamma da yankin Sahel ya fitar ya nuna cewa a watan Yulin da ya gabata an samu ƙaruwar satar mutane domin kuɗin fansa a Najeriya idan aka kwatanta da Yunin wannan shekarar.

Shugaban kamfanin Dakta Kabir Adamu, ya shaida wa BBC cewa a watan Yuli kaɗai, mutum kusan 1,035 aka sace amma kuma an samu raguwa na wadanda aka kashe.

Dakta Kabiru Adamu, ya ce bisa ga mizanin da suke aunawa a watan Yunin 2024 an sace mutum 468 yayin da a watan Yuli kuma aka sace mutum 1,035.

Ya ce,” Idan aka auna za a ga kari aka samu wanda ya rubanya adadin na baya ma, to amma dangane da mace-mace kuwa an ɗan samu ragi don ba wani mai yawa bane.”

Shugaban kamfanin na Beacon Consulting, ya ce da suka yi nazari sun ga akwai abubuwan da suka janyo haka, muhimmai kuwa su ne tasirin da taɓarɓarewar tattalin arziki ke yi ga ɓangaren tsaro.

Ya ce, ” Abu na biyu kuwa shi ne siyasa,wato ‘yan siyasa na amfani da matsalar tsaron suna ƙoƙarin cimma burinsu, sai kuma abu na ƙarshe shi ne matsalar zamantakewa a tsakanin jama’a kamar shaye-shaye da suka yi tasiri a ɓangaren tsaron.”

Dakta Kabiru Adamu, ya ce wani abu da suka lura kuma shi ne masu satar mutanen sun sauya yadda suke karɓar kuɗin fansa.

Ya ce, ” A da su kan buƙaci a ba su kudade masu yawa, to amma a yanzu sun sauya salo saboda yanzu jimilar kuɗaɗe suke buƙata, ma’ana idan suka haɗa mutane da yawa sai su buƙaci a basu kudadensu a tare.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *