An sassauta dokar hana fita a Kano domin sallar Juma’a

Spread the love

Gwamnatin jihar Kano ta sassauta dokar hana zirga-zirga a jihar Kano daga karfe 12 na rana zuwa karfe biyar na yammacin yau Juma’a domin a bai wa mutane damar halartar sallar juma’a.

Wata sanarwa da ta fito daga jam’ian gwamnatin jihar Kano ta ce dokar dai zata ci gaba daga karfe biyar na yammacin wannan rana har zuwa lokacin da al’amura za su daidaita.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *