An Shiga Fargaba Bayan Da Yara 18 Suka Ci Yayan Zakami A Unguwar Medile.

Spread the love

Wasu yara 18 da ake zargin sun yi, amfani da yayan Zakami, ta hanyar Soya wa da gishiri, sannan suka cinye a unguwar medile karamar hukumar Kumbotso Kano, ya sanya su yin maye da harbin iska tamkar mahaukata.

Idongari.ng, ta ruwaito cewa, yaran sun debo yayan zakamin dake sanya maye, wadanda suka yi tsammanin zobe ne, da wasu ke soya yayan da gishiri ana siyar wa don ci.

Daya daga cikin iyayen yaran ta bayyana damuwarta, sakamakon faruwar lamarin da suka shiga na tashin hankali, wanda har sai da aka kai yaran na su asibiti aka duba lafiyarsu.

Abubakar Dangaladima, ya bayyana cewa yaran sun zata yayan Yakuwa ne, da wasu mata ke soyawa da gishiri, su kuma suka debo zakamin ba tare da sanin ko menene ba.

Ya kara da cewa sai cikin dare alamu suka bayyana cewar yaran suna cikin maye, kuma sun kaisu asibitin kwararru na Murtala Muhammed, inda aka duba lafiyarsu.

Rahotanni na cewa hankula sun tashi sosai, amma daga baya al’amura suka daidaita bayan da likitoci suka duba lafiyar yaran 18 , da yanzu haka sallame su kamar yadda idongari.ng, ta ruwaito.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *