Koriya ta Kudu ta auka cikin wani rikicin siyasar da ba a fiya gani ba, bayan katsam shugaban kasar ya ayyana dokar soji.
Shugaba Yoon Suk Yeol na zargin ‘yan hamayya da masu yi wa ƙasa zagon ƙasa da aikata laifuka.
Sai dai kuma kasa da sa’oi biyu ‘yanmajalisar dokokin kasar na jam’iyyar hamayya – wadda ke da rinjaye a majalisar – suka ki amincewa da matakin shugaban kasar.
Sun hallara a zauren majalisar inda suka kada kuri’ar da za ta dakatar da dokar.
Wasu daga cikin ‘yan kasar da suka fusata da dokar sun haura shingayen da aka sanya yayin da wasu kuma suka tsallaka katanga don samun shiga cikin majalisar.
Sojojin Koriya ta Kudun dai sun ce za su tabbatar da umarnin shugaban kasar na amfani da dokar sojin har sai ranar da ya ɗage ta.