Rundunar yan sandan jahar Kano Kano, karkashin jagorancin kwamishinan ta, CP Salman Dogo Garba, ta shirya bitar kwanaki 2, ga limamai da Ladanan ofisoshin yan sanda da kuma na sauran hukumomin tsaron Nigeria, don kara tunatar da juna kan harkokin addinin musulinci musamman wajen isar da sako ta hanyar da ta dace da kuma yadda ake yin kiran sallah da kura-kuran da ake samu don gyarawa, inda aka gayyaci manyan Malamai don yi jami’an bita.
Babban Limamin masallacin jumma’a na shelkwatar rundunar yan sandan Kano, CSP, DR. Abdulkadir Haruna, ya bayyana cewa sun shirya bitar ce don kara dankon zumunci tsakaninsu da yan uwansu Limamai da Ladanai na sauran hukumomin tsaro, da kara tunatar da juna wajen yin Da’awah.
” a matsayin mu na daliban ilimi da muke dan kokari wajen kara tunatar da al’umma, yana da kyau mu dada kula da salon da muke amfani da shi, wajen isar da sako, domin malami sanda zai yi magana bai san mutane na wa ne ke sauraransa ba” cewar CSP Dr. Abdulkadir Haruna”.
Ya kara da cewa saboda haka ne suka ga da cewar su kara tunatar da junansu, musamman limaman da suke ofisoshin baturen yan sanda, don kyautata usulubi wajen isar da sako, sannan su kuma ladanai su kula da kiran sallah, domin yana da muhimmanci sosai saboda Manzon Allah ( S.A.W.) ya yi Hadisai ma yawa akai.
Limamin ya ce rashin sanin yadda za a furta lafuzzan daidai maimakon ya samu lada , sai ya samu laifi.
Ya kuma ce rashin bin usulubin da’awah, ya na haifar da rikicewar duniya, don mai yin wa’azi yakan furta wani abu da tunzura mutane, ko yin maganganun da shi kansa za su kama shi, domin harshe rabin dan Adam ne sauran rabinsa kuma zuciya ce.
” don haka idan mai wa’azi bai iya tsara usulubin yin wa’azinsa ba, maimakon ya zama ya fadakar , sai ya watsar da al’ummar ko yin magangunun da ya haifar da tashin hankali har akasa karbar sakon da zai isarwa da mutane”.
- Yan Sanda Sun Kama Wani Mutum Da Zargin Zuba Wani Abu A Rijiya A Kano.
- Yan Sanda Fara Kama Wadanda Suke Da Hannu A Fadace-fadacen Unguwanni A Kano.
Babban kwamandan hukumar hisbah na jahar Kano, Asheik Dr. Aminu Ibrahim Daurawa, ya daya daga cikin manyan malaman da suka bayar da bitar, inda ya bayyana cewa akwai bukatar duk wanda zai yi wa’azi yakamata ya siffofi da dabi’u da kuma halayen da zai siffantu da shi , wajen bin hanyoyin yi wa alumma wa’azi ba tare da kawo tashin hankali ba , tunda masu yin wa’azi suna bayar da gudunmawa wajen kwantar da tarzoma ba tayar da hankali ba.
Daurawa ya kara da cewa, ana bukatar wa’azi sosai amma son a dinga lura da wadanda ake yi wa wa’azin da yanayin da ake yin da kuma kalmomin da za a yi amfani da su don suyi tasiri ga jama’a don ya yi amfani.
” kuma daman Manzon Allah, da ya koyar da wa’azi , ya ce lallai ya ce masu wa’azi su dinga yin amfani da hikima” cewar Daurawa”
Dr. Kasim Ramadan Malami daga sashin koyar da addinin musulinci mai zurfi , a jami’ar Northwest Kano, ya gabatar da bitarsa kan yadda ake kiran Sallah da kuma kuraran da ake samu wajen chanja ma’ana.
ya ce wajibi ne ladani ya zama mai kula da lokaci , gaskiya, ilimin sanin harshen larabci wajen fitar da dukkan sautukan yadda suke, don kaucewa chanja ma’ana” inda har wasu malamai na cewa duk kuskuren da kaa samu wajen chanja ma’ana to kiran sallah ya baci”.
Dr. Ramadan ya kara da cewa taron bitar da aka yi yana da matukar muhimmanci ga ladanai da kuma sauran wadanda suka halacci bitar.
Kwamishinan ma’aikatar addinai na jahar na Kano, Sheik Ahmad Tijjani Auwal, ya bayyana farin cikinsa dangane da bitar , musamman yin hakan zai kara samar da tsaro a cikin al’umma.
Ya kuma yi kira ga sauran jami’an tsaron da suka amfana da su ci gaba da yada ilimi a cikin al’umma, inda ya tabbatar da cewa gwamnatin Kano, a shirye ta ke don tallafawa jami’an tsaron a koda yaushe.
Kwamashinan yan sandan jahar Kano, CP Salman Dogo Garba, wanda ya samu wakilcin Mukaddashin kwamishinan yan sanda, DCP Umar Ahmed Cusso, ya godewa dukkan wadanda suka bayar da gudunmawa musamman malamai wajen kara ilimantar da Limaman masallatan da kuma ladanansu, inda ya yi fatan za a yi amfani da abunda aka koya.
An fara gabatar da taron bitar na yini biyu daga ranar Laraba zuwa Alhamis, inda aka samu halattar hukumomin tsaron, yan sanda, Civl Defense, Road Safety, Sojoji, jami’an gidan gyaran hali , Karota da dai sauransu, inda aka ba wadanda aka yi wa bitar shaidar halattar taron.