An soma rayuwa a duniya fiye da shekara biliyan ɗaya da rabi – Tawagar masana

Spread the love

Wata Tawagar masana kimiya ta ƙasa da ƙasa ta ce ta gano wasu sabbin shaidu da ke tabbatar da cewa an fara rayuwa a duniya, fiye da shekara biliyan ɗaya da rabi da aka yi tunani a baya.

Tawagar masanan ta ce ta gano hakan ne daga ƙasar da ke cikin wani dutse mai zurfi a Gabon da nahiyar Afirka.

Sun ce sun gano fashewar abubuwan da ake buƙata don tallafa wa ƙwayoyin hilitta da suka ƙunshi iskar Oxygen da suka kai sama da shekara biliyan biyu.

Ɗaya daga cikin masanan daga Jami’ar Cardiff a Wales ya shaida wa BBC cewa yanayin ba ya taƙaita ne a wani ƙaramin yankin don haka ba duka masanan ba ne suka amince – sun ce akwai buƙatar samun ƙwararan hujjoji.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *