Wasu mabiya shafukan sada zumunta musamman Facebook, sun tafka muhawara, kan wata amsar tambaya da kakakin rundunar yan sandan jahar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya yi bayan wata budurwa, ta nemi shigar da korafin ta kan samarin da suka yiwa yan matansu, alkawarin fitowa don ayi mu su baiko kafin watan Disambar 2024 ya kare, amma ba suka ki fitowa.
SP Abdullahi, ya wallafa tambayar da matashiyar budurwar ta yi masa da cewa” Wata ta tambaye ni wai akwai sashin da ake karbar korafi a Bompai, akan samari wadanda suka ce za su fito kafin Disamba amma ba su fito ba? Amsa: Babu, sai dai a tafi Kotu.
Rundunar yan sandan ta ce babu wani sashi da aka ware don karbar korafin yan mata , kan samarinsu da suka yi mu su alkwarin fitowa don a yi baiko musu baiko, sai dai rundunar ta ce suna damar zuwa kotu don shigar da kararsu.
Wannan wallafa dai ta sanya mutane da dama musamman samari , yin martani kamar haka.
Sagir Danladi Usman Ai ma su wannan tambayar suna da yawa, ni ma zan kai wata yarinya kara taki yadda na fito.
Bashir Sani Ni kaina akwai wacce nai wa irin wnn alqawarin, yanzu haka na jefa ta a “black list” naje Whatsapp ma na buloke ta. Na tabbatar wnn yarinyar idan ta samu dama zata iya miqani koda barikin sojoji ne.
Sule Ya’u Tariwa Ya dai kamata a kirkiri Department na musamman. Ko bulala ne a rinka yima samarin shaho, masu cewa sai December.
Yahaya Lawan Gadanya A duba lamarin a daura dakai kafin January
Muazzam Madaki Hahhhhh yadai kamata a duba korafin ta.
Sani Usama Bagari Funtua Officer kufa abokan kowa ne
Kamalu A Muhammad Ranka ya daɗe ba fitowar ce ba sa son yi ba, bata yiwuwa ne saboda halin ƙuncin rayuwar da ake ciki. Gashi kuma mutane sun ɗorawa kansu abubuwan da ba Allah ya ɗora musu ba a kan aure. Mu ragewa kanmu ko ma samu sassauci.
Mubarak Aminu Yakubu ·
Idan na kama dan sanda ya aikata laifi zan iya kama shi na kawo shi ofishin ku?
Ismail Auwal Sarki
Ai kuwa da an bude a wannan satin cika zeyi taf wajan saboda yawan masu kaho korafin.
Muhammad Bello MAN SAGIR, SUJE HISBA KAWAI WAJEN SHEIKH DAURAWA AKWAI SASHIN ACEN EH.
Aliyu Abdullahi Cisse ·Lallai ya dace ace akwai wannan officer din a bompai saboda a rika hukunta masu shaka tafi
Zainab Ishaq Muhammad
Maganar gaskia ban ji dadi ba, don har na tattara hujjoji zan kawo sunan wasu mutum 3, duka alqawalin Disamba sukayi min amma shiru
, daya ma da nayi bincike wai ya tafi Libya neman kudi.
Usman Shuaib Bosha Akwae sashin da ake karɓar ƙorafi na kyawawan matan da babu halin kula su?
Aliyu M. Ahmad Idan budurwa ko saurayi ya yaudare ku, za ku iya shigar da ƙara KOTU, a yi musu hukuncin ɗaurin shekara 1, tare da tarar ₦200k a dokar Nijeriya.
MJ Dawanau
Assalamualaikum! Ranka ya dade, a tura su Hisba, Malan Yayi musu nasiha, idan aka dace, sai a daura auren a gaban malam. Domin Ni nasan kudine ya hana su fito. Maza sun daina yaudara, amma suna gudun high bill .
Ishaq M Ishaq Gaskiya yakamata ku bude wannan sashin sai a hada Dana karbar korafi akan Yan matanda suka yaudari samari.
Koguna Magaji
Muna December BA sai anje kotuba kara basu hakuri saura Kada.
Umar Farouk
Boss. Yakamata a fito da sashin da take magana akai
.
Muhammad Musa Sale ·
Don in mentioned na suna zanyi sati yayi kadan in gama zaiyano sunayensu.
Gen Sunusi Alhamdulillah Na tsallake rijiya da baya kenan…
Zawarawan da nacewa zan fito on December sun fi 5.
Usman Nuhu Abubakar
Oga tunda wannan civil case ne, Ayi mata jagora zuwa Sharia court bamanaki Alkali ya daura musu aure acan Ayi gaba daya a huta
Musbahu Suarjo Yallabai ai har yanzu December bai kare ba ace mata ta kara hakuri
Abubakar Basiru Jibaga
Allah mun gode maka, da tuni qila an dasa mana camera ana ka daga murya dakyau, shekarunka nawa ?
Queen Meera Dadai an Kara duba lamarin
Dan tun daga habuja zan kawo nawa korafin kano.
Ummu Safiya S Inuwa ·Wan Nan shakiyanci dayawa yake
Allah yasa su turo cikin disambar din ko bayan disamba.
Fateema Kurawa Ja’iri yasamu wadda ta fishi jarfa
idan ansan kotun data kai ayi tagging dina.
Hamza Imam Kano Rashin sani ne yasa samari ke tsoron aure a shekarun baya, yanzu ne ya kamata aji tsoron aure
dan ko kana da sana’a sai ka haɗa da addu’a
Sabo Kalaboda Saidu
Toh gaskiya yakamata a bude wannan sashin domin yima yan uwa nisa’u adalci an jima ana yaudarar su da December za’a tura.
Buhari Dalhatu ·
Anya kuwa
yallaɓai kodai kaima akwai wacce kayiwa alƙawarinne kake jin tsoro
Iliyasu Dahiru
Yallabai nima wata ta yaudareni,an daura mata aure jiya ina xankai kokena pls
Umar Muhammad Jega Muhammad
oga wane hukunci zaku Tanada nan Gaba akan masu yi muku tambaya maras ma,ana?
megirma sp da gaske Ana saida shin kafa da wake a bompai
Nuraddeen Abdallah
Gaskiya yakamata asamu wannan sashin domin suma masu yaudara masu lefi ne kuma kune kuke d alhakin kama masu lefi.
Sadeeque Adam Sardauna Oga gwara fa a Bude sashin a wajenku don zamu iya sasantawa amma kotu Kuma ana Zama kalau
.
Mannir Auwal Maikusa
Watan a baya mata sun yaudari samari son ran su,basu San irin radadin da ake jiba Sai yanzu a Abun ya juya kansu…… Samari Kuna sha’anin ku ama kuji tsoran Allah.
Aliyu Nuhu Sallau
Mai Girma Sp Ina da aboki Mai irin wannan dabi’ar, da ace zaku kokarta duk irin wadannan baragurbin samarin a kama su a antaya su a magarqama ko babu komai gani ga wane zai ishi wane tsoran Allah.
Idris Kassim Aliyu Bisa kuɗirin maigirma kwamishinan ‘yansandan jihar Kano CP Salman Dogo Garba, wanda jama’a su ka yi wa laƙani da “Dogon Aiki” kuma kwamishina na arba’in da shida a wannan jiha. Na tabbatar da kiyaye haƙoƙin mutane da hana samari yaudara, to yau dai Allah ya bamu Nasara…. Rahoton da muka samu kan Samarin dake cewa za su fito kafin Disamba, amma yanzu Disambar na neman ƙarewa babu su babu labarin su, dan haka nake cewa wannan case yafi ƙarfin mu sai dai Supreme Court.
Asalin BakatsineMuna Alfahari da wannan jinsin namu
Allah yakara doraka akanta kaci gaba da gana mata azaba
Zainabu AbuTo akwai sashi masu kula da samari masu zuwa zance empty hand
Don Allah a temaka ai reffering dina.
Edreeth Hudu Bichi
Gaskiya yallabai a duba lamarin ta wata kila ta kori wasu ne tanatinanin cewa shi zai fito December
Abdullahi Haruna Kiyawa
Yallabai adai duba lamarin.
Usman Giovani Ya kamata a fara karɓar irin wannan korafin gaskiya.
Khadija S Aminu
Yallabai yakamata a Bude sashi na musanman domin hukunta maza mayaudara, aduba wanan koken ranka yadade
Nazirun Jarumi Rano Haba Yallabai Ai kamatayi Ace akwai sai abunchika daganan idan ba’a tabbatarba sai Aturasu kotu.
Sheikh’
Wai Dan Allah Oga Abdullahi Haruna Kiyawa Abokan aikinku Mata basu haihuwa ne, Allah ban taba ganin macen yar Sanda da Ciki ba …?
Abbas Lastdone
Yallabai gari ne fa yaci wuta
Ni kaina a yanda na tsara da komai ya tafi dai dai Yau 28 December itace ranan daurin aure na amma kaga dai yanda lamarin ya kaya
Yanzu hakama ina kasuwa na zubawa sarautar Allah ifo.
Aliyu Yahaya Isah
Yallabai aiku ya kamata ku karbii korafin daga nan sai ku tura kotun
Ina ganin hakan xaifii.
Suhaib Muhammad In da akwai irin wannan sashe ai da tuni ina Prison, don ni sama da shekaru 10 duk Disamba da alkawari take zuwa min.
Amman ina bawa Mata shawara shi Aure lokaci ne, ku daina takurawa Samari sai sun fito sun aureku wannan ne yasa suke muku ƙarya don a zauna lpy.
Bukhari Ashafa Yallabai tunda sabuwar shekara zamu shiga a sabbi doka da Za’a fitar ya kamata a saka wannan dan ayi maganin mayaudara.
Sulaiman Yusuf Muhammad Wannan abu yayi kyau da babu wannan sashen domin kuwa da akwai shi ko shakka babu zai wahala yau na kwana a gida domin kuwa nima nai wa wasu alƙawari.
Muhammad Ghali Baban Zahra Hhhh Ita wanda yace yana sonta taki shi shi kuma ina zai Kaita? Allah ne yake hukuntamu daidai da ayyukanmu Malama.
Musa Garba Musa
Shawara zuwa ga folisawa don Allah ku taimaka ku bude sashen da masoya wadanda aka yaudara zasu na kai korafi saboda yan matan nan basu da mutunchi wlh.
Muhammad Salees TK Yakasai Wacce kuma take da saurayi sama da Daya Sedai mu kaisu kotun majalisar Dunkin duniya Dan anan ba za’a Mana Adalci.
Usman Muhammad
Duk da cewa Yan Sanda sunyi sansani a Kofar Mata tsawon sati 2 ko sama da haka, amma tabbas bayyanar Jami’an Vigilante yau a kofar mata ya kayatar dani matuka, wadda a raina naji cewa Babu wani tsageran Yaron da zae iya wargi don tada hankalin Al’umma.
Saboda da ganin su kasan suma ba kanwar lasa bace, Allah ka zaunar mana da Garuruwan mu lafiya, ka zaunar da Nigeria Lafiya, ka bamu lafiya mai amfani da amfanar wa
A raina nake furtawa cewa ” Idan ciki bai koshin ba aikin pa ba zae yiwu ba, to yanzu idan sunji yunwa Wa zai basu abinci?” Can kuma nace ” Allah ya kawo wadda zae rika ciyar dasu tsawon lokacin da zasu dauka a wannan sansani don kuwa idan jiki yayi la’asar aikin ma bazae yiwu ba, karshe bacci zae kama mutum ne”.
Abinda Gwamnati take basu baya wadatar dasu da komae.
Allah ka karfafi duk wani mai son ganin al’umma sun zauna lafiya
.
Jamilu Ibrahim
Sai kaga yamata ai sai da hali me girma PPRO tunda ba da baki ake ba.. Allah SWT Ya horewa bayinSa.
Khamis Aminu Abubakar Kabo
Yallaboi nima wata baiwar Allah tasani tsaka Mai wuya
Kullum da ita nake tashi daga bacci, Kuma kullum Ina cikin tunanin ta
Inason aurenta Amman tace bazatayi aure yanzu ba
Menene abinda ya dace nayi yanzu
.
Bin Usman Indabawa
Ba laifi samari bane laifin manyan kasarmu ne saboda sun lalata mana gobenmu shiyasa wanyanda suka ce zasu futo disamba suka kasa fitowa.
Murtala Bachirawa
Humm Kawai kudaukesu aikin police xasu bada gudun mawa sosai kafin Allah ya kawo musu wasu.
Real Sani Idris
Oga kace Ina daya daga cikin masu zuwa kotu sbd Ina da wannan laifin.
Abubakar Saddiq Ibrahim
Gsky yakamata Aduba lamarin Abuda wannan sashen, Saikuyi bincike Idan kudine yahana mutum fitowa kawai kutaimakai da kudin yafito, Rundunarku agsky tana taimako Kuma tanada kudi, Idankuma kuka gano samarin shahone kiyi Mai buloli.
Shehu Umar Yunus Wuna
Allah Kabamu Lafiya da Zaman Lafiya, Kano da Nigeria Sune A Gaban Mu, Ka Karawa Yan Sanda Yawan Albashi Su Samu damar Kara Aure
Basheer Muhd Twd
Ranka Yadade Wlh Baku Da Gun Ajiye Masu Wannan Ire Iren Laifikan
Dan Haka Gwara Dakayimata Wayo
Abba Musa Jiyan
Officer wannan ma laifine ku kuma dama mai laifi kuke nema ,…. Amma ai disambar bai wuceba
Isah Abdu Yaro
Da kamar shekara 2 ne da ta shige da na haɗa ta da wani boka ya tilasta shi ya aure ta a ragowar kwanakin da suka rage sai dai yanzu Allah Ya shiryi bokon ya koma shaye-shaye da sai da wiwi.
Abbas Umar Yahya
Alhmdullih na tsalake rijiya da baya Kenna har naji kirjina yace wani tirissssssss
Uzairu Halidu Jani Rankai Dade ya kamata ku fara kama Samarin Shaho gaskiya!
Abdullahi Haruna Kiyawaa.