An tsame manoma da ƙananan ƴan kasuwa daga harajin cinikayya a Najeriya

Spread the love

Gwamnatin Najeriya ta tsame manoma da ƙananan ƴan kasuwa da masu kamfanoni daga biyan haraji na cinikayya.

Shugaban kwamitin shugaban ƙasa kan yi wa haraji garambawul a Najeriya, Taiwo Oyedele ne ya sanar da matakin a shafinsa na X.

Ya ce muhimman sauye-sauyen da aka yi za su magance matsalolin da aka gano da kuma sanya masu ƙananan sana’oi cikin waɗanda aka tsame daga biyan harajin cinikayya, tsame masu kamfanoni da masu sarrafa kayayyaki kamar manoma: matakan da za su magance kauce wa biyan haraji.

Ya ce an bijiro da tsarin harajin a Najeriya a 1977.

An tsara shi ne domin bai wa gwamnati damar samun kuɗaɗen shiga a kai a kai tare da zama wata dama ta magance kauce wa biyan haraji, in ji kwararren kan haraji.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *