Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta ce ta tsaurara matakan tsaro a wasu ƙananan hukumomin jihar da za a sake gudanar da zaɓen cike gurɓi a ranar Asabar.
A ranar Alhamis ne Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Kayode Egbetokun ya sanya dokar hana zirga-zirga daga karfe 12:00 na rana zuwa 6:00 na yamma, a yankunan da ke cikin jihohi 26 na kasar inda za a gudanar da zaɓen cike gurɓin.
Rundunar yan sandan Nigeria shiya ta , Kano da Jigawa ta bayyana shirin ta na zaben ranar Asabar.
Da yake yin karin haske, mataimakin sufeton ‘yan sanda na jihar Kaduna, Mansir Hassan, ya lissafa kananan hukumomin da al’amarin ya shafa da suka hada da Chikun da Igabi da Kachia da Kaduna ta Kudu da Kagarko da Kudan, da kuma Kauru.
A cewar wata sanarwar da aka fitar, kakakin ‘yan sandan ya ce za a aiwatar da cikakkyar dokar hana zirga-zirga daga tsakar daren Asabar, 3 ga Fabrairu zuwa 5 na yamma.
Sai dai ya ce muhimman ma’aikata da suka hada da jami’an hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) da masu sa ido kan zabe da ma’aikatan lafiya da kuma jami’an yaɗa labarai da aka amince da su su ne kawai dokar ba ta shafa ba saboda muhimmancin aikinsu..
Rundunar ‘yan sandan ta yi gargadin cewa ba ta son ta ga wadanda ba su da izinin a cibiyoyin rajista (RAC), da rumfunan zaɓe, da wuraren tattara sakamakon zaɓe, inda ta yi gargadin cewa mutanen da ke da niyyar tayar da hankali to za su fuskanci kame sannan kuma a gurfanar da su gaban kuliya.