An tsige mataimakin shugaban ƙasar Kenya

Spread the love

Majalisar dattawa ta ƙasar Kenya ta tsige matamakin shugaban ƙasar Rigathi Gachagua.

Shugaban majalisar ya ce sanatoci sun tabbatar da tuhume-tuhume biyar daga cikin 11 da aka gabatar a kan tsohon mataimakin shugaban ƙasar, waɗanda duka ya ƙaryata.

Daga cikin laifukan akwai raba kan al’umma da saɓa dokokin aikin ofis ɗinsa da kawo tsaiko a aikin tattara bayanan sirrin ƙasar.

Rigathi Gachagua mai shekara 59 ya yi iya bakin ƙokarinsa domin hana tsigewar, sannan ko a yammacin yau lauyansa ya ce ba zai samu halartar zaman majalisar ba saboda yana kwance a asibiti, har ya buƙaci a ɗage zaman, amma sanatocin suka ƙi amincewa, inda suka cigaba da tattaunawa ba tare da yana nan ba, har suka kai ga tsige shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *