Majalisar Dokokin Jihar Legas ta tsige shugabanta, Honorabul Mudashiru Obasa, daga kujerar shugabancin, inda ta maye gurbinsa da Honorabul Mojisola Meranda, mai wakiltar Mazabar Apapa I.
Majalisar ta kuma zabi Mataimakin Shugaban Mai Tsawatarwar, Fatai Mojeed, a matsayin mataimakin shugaban majalisar.
Takun sakar Obasa da majalisar ta fara ne tun bayan da kalaman da ya yi kan aniyar takarar zaben gwamna a shekarar 2027.
- Hukumar ƙwallon ƙafa ta Najeriya ta gabatar da sabon kocin Super Eagles
- Rundunar Sojin Saman Nigeria Za Ta Yi Bincike Kan Zarginsu Da Kashe Fararen Hula A Zamfara