An Tura Kwararrun Yan Sanda Don Kubutar Da Daliban Da Aka Sace A Benue

Spread the love

Babban sifeton ‘yansandan Najeriya, Kayode Egbetokun, ya bayar da umarnin tura ƙarin ƙwararrun jami’an rundunar zuwa jihar Benue don taimakawa wajen kuɓutar da ɗaliban jami’ar da ‘yan bingida suka sace a jihar.

A ranar Alhamis ne wasu ‘yan bindiga suka sace ɗaliban jami’ar Maiduguri da ta Jos, waɗanda ke kan hanyarsu ta zuwa jihar Enugu domin halartar wani taron shekara-shekara.

Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yansandan ƙasar, Muyiwa Adejobi, ya fitar ranar Lahadi, ya ce Egbetokun ya bayar da umarnin tura ƙwararrun jami’an da kayan aiki, ciki har da jirage marasa matuƙa da masu saukar ungulu da motocin sulke domin tabbatar da kuɓutar da ɗaliban.

Mista Egbetokun ya kuma yi kira ga mazauna yankin su bayar da bayanan da za su taimaka wajen kuɓutar da ɗaliban.

Ya kuma jajanta wa iyalan ɗaliban tare da alƙawarta kuɓutar da su.

”Rundunar ‘yansanda na tare da iyalai da ‘yan’uwan ɗaliban a wannan lokaci na baƙin ciki da damuwa, kuma rundunarmu za ta yi duk mai yiwuwa domin kuɓutar da waɗannan ɗaliabi”, in ji sanarwar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *