Babban Sufeton ƴan sanda na Najeriya, Kayode Egbetokun ya yi kira kan ƙara tsaurara matakai domin yaƙar masu garkuwa da mutane da sauran masu aikata miyagun laifuka a Abuja, babban birnin ƙasar.
Babban Sufeton ya yi magana ne jiya Talata bayan taron da ya yi da rundunoni na musamman da ke yaƙar laifuka a Abuja game da ƙaruwar matsalar tsaron da babban birnin ke ciki.
“Ya bayyana damuwarsa matuƙa kan abubuwan takaicin da suka faru sannan ya jaddada buƙatar ɗaukar matakan da za su kawo ƙarshen waɗannan miyagun laifuka” a cewar kakakin rundanar ƴan sanda ta ƙasa, Muyiwa Adejobi.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa a taron da ya mai da hankali kan nazarin ƙalubalan tsaro da ake fuskanta yanzu da kyawawan tsare-tsare da kuma samar da kayan aiki domin shawo kan barazanar da ke ƙara ƙaimi, Babban sifeton ya jaddada buƙatar bin tsarin haɗin gwiwa da kuma tattara bayanan sirri domin shawo kan matsalar tsaron.
Shugaban ƴan sandan ya umarci mataimakinsa da “ya ja ragamar fito da dabarun kawo ƙarshen masu garkuwa da mutane da sauran masu aikata miyagun laifuka a birnin na Abuja tare da dawo da zaman lafiya nan take”.