An Wawashe Kayan Abinci A Ma’ajiyar Gwamnatin Jigawa

Spread the love

Wasu mutane da ke iƙirarin zanga-zanga sun auka wa wuraren ajiyar abinci na gwamnatin jihar Jigawa da ke arewacin Najeriya tare da wawashe kayan ciki.

Wani shaida ya faɗa wa BBC cewa wuraren ajiyar uku masu zanga-zangar suka far wa.

“Jami’an tsaro suna kallo aka fasa wurin saboda masu zanga-zangar sun fi ƙarfin su,” a cewar Umar Ibrahim da ya shaida lamarin.

Ƙaramar hukumar Birnin Kudu na da nisan kilomita 43 daga Dutse babban birnin jihar, inda jami’an tsaro suka harba wa masu zanga-zanga hayaƙi mai sa hawaye da safiyar yau Alhamis.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *