An Yanke Wa Malamin Jami’a Na Bogi Hukuncin Daurin shekaru 6 A Kano.

Spread the love

Babbar Kotun Shari’ar addinin musulinci dake zaman ta, a Garin Bichi Kano, ta yanke hukuncin daurin shekaru 6 ga wani mutum da aka samu da laifin bayyana kansa a matsayin malamin jami’a, ta hanyar kwace wayoyin Hannun daliban.

Jami’an Yan Sandan Kano ne Suka Gurfanar da shi, bayan da Suka samu korafe-korafe daga makarantar FCE Kano, da kuma jami’ar Ilimi ta Sa’adatu Rimi Kumbotso, da cewar malamin bogi Yana shiga dakin karatun dalibai ya bayyana mu su cewar shi ne sabon malamin su da zai ci gaba da koyarsu.

Idongari.ng, ta ruwaito mu ku cewa , Lakcharan bogin yana yaudarar Daliban ta hanyar Yi mu su jarrabawar gwani, Inda yake karbe wayoyin su don karsu saci amsa, Amma sai ya bar Daliban a cikin aji suna rubuta jarrabawar gwani , ya gudu da wayoyin.

DANDALIN KANO FESTIVAL

An kama Wanda Ake Zargin ne a jami’ar Ilimi ta Sa’adatu Rimi Kumbotso, lokacin da ya sake koma don yaudarar wasu daliban Inda dubunsa ta ciki.

Bayan karanta masa kunshin tuhumar da ake Yi masa amsa laifinsa.

Alkalin kotun shari’a Malam Kabiru Idris Sadik Fagge, ya yanke masa hukuncin daurin shekaru Uku a gidan ajiya da gyaran hali da tarbiya ko biyan tarar naira Dubu Talatin 30.000. a laifin da ya aikata a makantar FCE Bichi.

Haka zalika an yanke masa hukuncin daurin wasu shekaru ukun bisa Samun da laifi a jami’ar Ilimi ta Sa’adatu Rimi Kumbotso, ko kuma zabin biyan tarar naira Dubu saba’in 70.000 sannan kuma zai biya kudin rankon wayoyin Hannu naira Dubu dari da biyar 105,000.

Idongari.ng, ta Nemi jin ta bakin wanda aka yanke wa hukuncin Amma yaki cewa komai, kuma tuni jami’an gidan ajiya da gyaran hali da tarbiya suka tafi da shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *