Wata babbar kotu da ke jihar Kwara a kudu maso yammacin Najeriya ta yanke wa Abdulrahman Bello, wanda ya kashe masoyiyarsa Yetunde Lawal hukuncin kisa ta hanyar rataya.
An zargi Abdulrahman da laifin kisan matashiyar yar shekara 23, kuma dalibar kwalejin ilimi na jihar Kwara da ke Ilorin a watan Fabrairun 2025.
Yan sandan jihar sun kama matashin ɗan shekara 29 bisa zarginsa da kashe ta da kuma daddatsa gawar ta.
Mai shariah Hannah Ajayi ce ta yanke hukuncin bayan kotun ta tabbatar da laifin da ake zarginsa da shi, inda ta ce shaidu sun nuna Bello ya kashe Yetunde ne domin ya yi amfani da gawar ta wurin yin tsafi, ya kuma sayar da sassan jikinta.
A cewar Hannah Ajayi, soyyayar da yake mata da alƙawarin aurenta, ƙarya ne, kuma ya yi mata su ne da nufin yaudarar ta ta je gidansa domin ya kashe ta.
Ƴan sandan jihar sun bayyana cewa Yetunde ta ɓace ne a ranar 10 ga watan Fabrairu, kuma bayan kwana huɗu aka gano gawar ta a gidan wanda ya kashe ta.