Rundunar yan sandan jahar Kano, ta bayyana cewa an yanke wa matasa 106 hukunci,wadanda aka same su da aikata laifukan daba, bayan rundunar ta gurfanar da su a gaban wasu kotunan majistiri da ke Jahar, ya yin da ake ci gaba da shari’ar mutane 43, wadanda ake tuhuma da aikata manyan laifukan, kisan kai, garkuwa da mutane, fashi da makami da kuma samar da mummunan rauni.
Kakakin rundunar yan sandan jahar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya aike wa da idongari.ng, da yammacin Alhamis din nan.
Sanarwar ta ce an gurfanar da matasan ne, a kotuna daban-daban bisa jagorancin, justice Aloma M. Mukhtar da Justice A. B. Wali, dake zaman su rukunin kotuna na Nomand-sland da kuma Gyadi-Gyadi.
A ranar 4 ga watan yunli 2024, ne Rundunar ƴan sandan jahar Kano, ta yi Holen mutane 149 kan zarginsu da aikata laifukan, fashi da makami, kisan kai, Daba da garkuwa da mutane cikin kwanaki 10 da ya kama aikin da sabon kwamishinan yan sandan jahar ya yi CP Salman Dogo Garba.
Rundunar ta gurfanar da su bayan kammala bincike da ta yi , kuma yanzu haka an yanke wa mutane 106 hukunci ba tare da zabin biyan tara ba, ya yin da ragowar 43, suke ci gaba da fuskantar shari’a.
Akarshe sanarwar ta ce rundunar za ta ci gaba da jajircewa wajen yaki da aikata miyagun laifuka a fadin jahar.
- Chuchu: Kotu Ta Hana A Gwada Ƙwaƙwalar Matar Da Ta Kashe Yaron Gidanta
- Shugabannin ƙwadago sun isa fadar shugaban ƙasa don ganawa da Tinubu