An yanke wa wani mutum hukuncin kisa kan tayar da gobara a Japan

Spread the love

An yanke wa wani ɗan kasar Japan hukuncin kisa bisa samunsa da laifin tayar da gobara a wani ɗakin shirya hotuna masu motsi na Kyoto animation a shekarar 2019 wanda ya kashe mutane 36 tare da jikkata wasu da dama.

Lamarin ya kasance ɗaya daga cikin mafi muni cikin shekaru na baya-bayan nan wanda aka rasa mafi yawan matasa masu fiƙirar zane da kuma girgiza duniyar shirya hotuna masu motsi.

Shinji Aoba, mai shekaru 45, ya amsa laifin kai harin amma lauyoyinsa sun nemi a yanke masa hukunci mai sauƙi inda suka yi iƙirari cewa yana da matsalar ƙwaƙwalwa.

Amma alƙalan sun ƙi amincewa da buƙatarsu inda suka ce Aoba ya san abin da yake yi.

“Na tabbatar da cewa wanda ake tuhuma bai da wata matsalar ƙwaƙwalwa ko rauni a lokacin daya aikata laifin”, in ji Babban Alƙali Masuda a ranar Alhamis a wata kotu da ke yankin Kyoto.

“Mutuwar mutum 36 abu ne mai tsanani da ban takaici. Fargaba da kuma raɗaɗin waɗanda suka rasa ransu a gobarar ba zai kwatantu ba”, in ji shi a cewar rahotannin NHK.

Yansanda sun kama mutum takwas da suke zargi da sace ɗaliban Ekiti

An kashe da yawa daga cikin ma’aikatan dakin shirya hotuna masu motsi bayan sun maƙale a saman bene na ɗakin yayin da gobarar ke yaɗuwa.

Wannan da ɗaya daga cikin al’amuran da suka fi tayar da hankali a cikin ‘yan shekarun nan a Japan, lamarin dai ya haifar da makoki na kasa. Jama’a da kafofin yada labaran ƙasar sun yi ta bibiyar lamarin sosai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *