An Yankewa Mutumin Da Aka Samu Da Laifin Yi Wa Yarinya Fyade Hukunci A Kano.

Spread the love

Babbar kotun jahar Kano Mai namba 1, dake sakatariyar Audu Bako, karkashin jagorancin Justice Dije Abdu Aboki, ta yankewa Wani Mai suna Ado Idris, hukuncin daurin shekaru 19 , sakamakon samun sa da laifin Yi wa, wata karamar yarinya Fyade.

Mai gabatar da kara, lauyar Gwamnatin jahar Kano , Barista Fatima Ado Ahmed, ta gabatar wa da kotun shaidu guda 5.

A bangaren Wanda Ake tuhumar ya kare Kansa .

Sai dai Mai Shari’ar ta Yi karatun baya, Inda ta yanke masa hukuncin daurin shekaru 19 a gidan ajiya da gyaran hali da tarbiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *