An yi amfani da sa hannun Buhari na bogi don cire dala miliyan 6.2 a CBN’

Spread the love

An ci gaba da shari’ar da ake yi wa tsohon gwamnan babban bankin Najeriya CBN, Godwin Emefiele a babbar kotun tarayya da ke Abuja, inda aka tabbatar wa kotu cewa binciken kimiyya ya nuna cewa an yi amfani da sa hannun bogi na tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari wajen cire kuɗi dala miliyan 6.2 don daukar nauyin masu sanya idanu na ƙetare a zaɓukan ƙasar.

Wani shaida da EFCC ta kira, mai suna Bamaiyi Meriga ya tabbatar wa kotu ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Hamza Mu’azu cewa binciken kimiyya da aka yi wa takardun – da aka sanya hannu a kansu don cire kudin – ya nuna cewa sa hannu da hatimi da aka yi amfani da su wajen cire kudin ba daidai suke da na ainihi ba.

Ya kuma tabbatar da cewa sa hannun ba na tsohon shugaban najeriya Muhammadu Buhari ba ne, kuma ba na tsohon sakataren gamnatin tarayya, Boss Mustapha ba ne.

An gabatar wa alƙalin da ke jagorantar shari’ar takardun biyu, masu ɗauke da umarnin shugaban ƙasa a matsayin shaida, sannan kuma ya amince da su.

Yansanda sun kama mutum 254 bisa zargin garkuwa da mutane a Najeriya

Kwamitin da IGP Kayode Adeolu, Ya kafa Ya gano Mutane 300 a gidan yarin Kano, wanda babu kundin laifukan da Suka aikata.

Bayan da lauyoyin Emefiele suka nuna ƙorafinsu game da takardun, shaidar ya ce shi ba ma’aikacin EFCC ba ne kuma ba hukumar ce ke biyan sa ba.

Lauyan Emefiele, Matthew Burkaa, ya nuna rashin amincewarsa da shaidar, yana mai cewa shaidar ya yaudari kotun ne don kauce wa tambayoyin da za a yi masa.

To sai dai lauyan masu shigar da ƙara, Rotimi Oyedepo, bai ji dadin kalaman lauyan wanda ake ƙarar ba.

An dai ɗage shari’ar zuwa ranar 1 ga watan Maris domin ci gaba da shari’ar.

Emefiele na fuskantar shari’a a kotun kan laifuka 20 da suka ƙunshi zargin cin hanci da haɗin baki da cin amana da amfani da sa hannun bogi wajen cire kudi har dala 6,230,000.

Ana zargin sa da sa hannun bogi na tsohon sakataren gwamnatin ƙasar Boss Mustapha wajen ciye kuɗin ta hanyar da ba ta dace ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *