An ɗaure ƴar fim saboda yin liƙin kuɗi lokacin biki

Spread the love

An yanke wa wata ƴar fim ɗin Najeriya hukuncin ɗaurin watanni shida a gidan yari, bayan da aka ɗauki hotonta tana liƙa sabbin takardun kuɗin naira da aka fitar a bara, tare kuma da taka su .

An kama Oluwadarasimi Omoseyin ne a watan Fabrairun da ya gabata a Legas bayan faifan bidiyon ta a wurin wani biki da ya bayyana a intanet.

An kuma nuna ƴar fim din tana almunbazaranci da sabbi kuɗaɗen.

Da farko, ta ƙi amsa laifin da ake tuhumar ta da shi, amma daga bisani ta amsa laifin.

Gwamnatin jihar Oyo ta rufe coci saboda damun maƙwabta da hayaniya

Rundunar yan sandan Nigeria shiya ta , Kano da Jigawa ta bayyana shirin ta na zaben ranar Asabar.

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasar, EFCC, ta ce an ɗauki bidiyon tauraruwar ne da kuɗi kimanin naira 100,000 a lokacin da take liƙawa wajen daurin auren abokiyarta a unguwar Lekki da ke birnin Legas, shekara daya da ta wuce.

A jawabinta ga hukumar, Omoseyin ta ce ta karbi sabbin takardun naira ɗin ne daga wajen masoyanta a wurin bikin kuma ba ta san wadanda suka ba ta kudin ba.

A lokacin da ta bayyana a gaban kotu a ranar Alhamis, Omoseyin ta amsa laifinta bayan wasu “shaidu masu ƙarfi” da ake tuhumar ta da su, kamar yadda hukumar EFCC ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafin X.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *