Ana azumi kan tsadar rayuwa a jihar Borno

Spread the love

Wasu ‘yan Najeriya da dama a jihar Borno da ke arewa maso gabashin ƙasar sun fara azumi bayan da gwamnan jihar, Babagana Zulum ya yi kira da a roƙi “agaji daga Allah” kan matsalolin tattalin arziki da na tsaro da kuma kan tsadar rayuwa da ƙasar ke fuskanta.

A ranar Juma’ar da ta gabata ne Zulum ya buƙaci al’ummar jihar su gudanar da azumin kwana guda a faɗin jihar a ranar litinin sakamakon tsadar kayan abinci a kasar.

Bello Zabarmari, wani mazaunin jihar Borno, ya shaida wa BBC cewa shi da wasu da dama na azumi da addu’ar Allah ya warware musu matsalolinsu.

“Mun tashi da azumi a yau kuma da fatan Allah zai amsa mana addu’o’inmu nan ba da jimawa ba, gwamnan ya yi abin da ya dace da kiran mutane da su yi azumi,” inji shi.

Shari’ar Murja Kunya: Hukumar Hisbah a Kano ta musanta labarin da ake yada wa kan murabus din kwamandan ta Sheik Aminu Ibrahim Daurawa

Yan sandan Kano sun mika wa hukumar Hisbah matasa 38 da aka kamo a kwanar Gafan ciki harda ma su juna biyu da ma su shayarwa.

Umar Shehu, wani mazaunin da ke aiki da hukumar kashe gobara ta jihar, ya ce shi da abokan aikinsa ma suna azumin kamar yadda gwamnan ya umarce su.

‘Yan Najeriya dai na cikin wani yanayi na tabarbarewar tattalin arzikin kasar mafi tsanani a tarihi inda farashin kayan abinci da kayan masarufi suka yi tashin gwauron zabi a ‘yan watannin nan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *