Ana binciken gano waɗanda suka ciri miliyoyi a bankin Ethiopia

Spread the love

Babban bankin kasuwancin Ethiopiya ya bai wa abokan hulɗarsa da suka ciri kuɗin da ya zarce wanda ke ajiye a asusunsu nan da ƙarshen makon nan su mayar da kuɗaɗen ko kuma su fuskanci shari’ah.

Kafafen yaɗa labarai a ƙasar sun ce fiye da dala miliyan 40 aka cira ko aka tura wasu bankuna a ranar Asabar da aka samu tangarɗa ta tsawon sa’oi a bankin na CBE.

A wata hira da BBC Newsday, shugaban bankin Abe Sano ya ce bankin ya gano akasarin hada-hadar da aka yi a lokacin da aka samu matsalar.

Da aka tambaye shi ko bankin zai kai rahoton waɗanda ba su mayar da kuɗin ba ga ƴansanda, Mista Abe ya ce “eh, eh sosai ma. Mun soma yin haka.”

Ya ƙara da cewa bankin zai ɗauki matakin shari’a kan waɗanda suka ƙi mayar da kuɗaɗen nan da ƙarshen makon nan”.

Za a gina babbar cibiyar lantarki mai amfani da rana a Najeriya

An ƙarkare binciken zargin zubar da ciki da sojojin Najeriya ke yi a asirce

“Babu yadda za su tsira saboda abokan hulɗarmu ne. Mun san su. Za a iya gano su kuma za su yi bayanin abin da suka yi,” in ji Mista Abe.

Wasu kwastamomin da suka kwashi kuɗi mai yawan gaske tuni sun mayar wa bankin, in ji Mista Abe.

Sai dai ya ƙaryata rahotanni cewa kwastamominsu sun kwashi dala miliyan 40 inda ya ce kuɗin bai kai yawan wanda aka kwasa ba amma za a tantance yawansu bayan an gama gudanar da bincike nan gaba a makon nan.

Mista Sano ya ƙara da cewa ana yin bincike saboda wasu kwastamomi 10,000 da suka tura kuɗi lokacin da aka samu matsala sun yi haka ne kan ƙa’ida.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *