Wani binciken BBC ya gano cewa kamfanin abincin maƙulashe na McDonalds ya gaza wajen hana cin zarafin wasu mutane tara da aka yi safararsu zuwa Ingila daga Jamhuriyar Czech.
Dukkanin mutanen na aiki ne a wuri guda na wani sashe na kamfanin kuma mutanen da suka kawo su Birtaniya ne ke karɓe albashinsu.
Kamfanin da sauran rukunansa sun gaza gano cewa ana amfani da mutanen ne wajen bautar zamani – ciki har da yadda ake biyan albashin mutanen tara a asusu guda, kuma kowanne mutum guda na aikin sa’o’i 100 a mako guda.
Ɗaya daga cikin ma’aikatan ya bayyana yanayin uƙubar da suka tsinci kansu, inda har yake cewa da ma mutuwa ya yi.
Kamfanin da abokan hulɗarsa, sun ce sun ƙaddamar da bincike domin gano irin waɗannan barazanar a nan gaba da kuma cewa suna aiki tuƙuru wajen taimaka wa kowane ma’aikancinsu da suka fuskanci alamar cin zarafi.