Ana fargabar gini mai hawa biyar ya ɗanne mutane da dama a Anambra

Spread the love

Ana fargabar cewa wani gini mai hawa biyar ya rufta tare da danne mutane da dama a birnin Onitsha, na jihar Anambra.

Rahotanni sun bayyana cewa ginin, wanda ba a kammala gina shi ba, ya rufta a safiyar yau Lahadi lokacin da masu aikin gini ke hawa na karshe.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa tuni aka tura motar Katafila zuwa wajen domin fara aikin fitar da mutanen da ake kyautata zaton gini ya danne su.

Zuwa yanzu dai ba a san musabbabin ruftawar benen ba, sai dai wani ganau kusa da yankin ya bayyana cewa an ceto wani mutum guda yayin da ake ci gaba da aikin ceto.

Gobara Ta Tashi A Tashar Lantarki Ta Ɗan Agundi A Kano.

Ramadan: Mun kaddamar da jami’an bijilanti na musamman don dakile aiyukan batagari a Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *