A yau ne Ƙotun Ƙolin Najeriya za ta yanke hukunci kan ƙarar da gwamnatin tarayyar ta shigar gabanta tana buƙatar jihohi su bai wa ƙananan hukumomin ƙasar ‘yancin gashin kai.
Tuni dai kotun da aike wa lauyoyin duka ɓangarorin da ke cikin shari’ar.
Gwamnatin Najeriyar dai ta maka gwamnonin jahohin 36 a gaban kotu inda ta ke ƙalubalantar su yadda suke take haƙƙin ƙananan hukumomi da ya danganci zaɓe da ba su damar amfani da kuɗaɗen gudanarwarsu.
Sai dai gwamnonin sun buƙaci kotun da ta yi watsi da wannan buƙatar da gwamnatin tarayya ta shigar.
Gwamnatin tarayyar na kuma son kotun ƙolin ta bayar da umarnin tura wa ƙananan hukumomin kuɗinsa kai tsaye daga asusun gwamnatin tarayya, kamar yadda kundin tsari mulkin ya tanadar.
A Najeriyar ƙananan hukumomin sun jima suna ƙorafin cewa gwamnonin jihohin ƙasar na riƙe musu kuɗaɗensu, lamarin da suka ce shi ke janyo musu rashin gudanar da ayyukan ci gaba a yankunansu.
Masana dai sun jima suna kiraye-kirayen bai wa ƙananan hukumomin ‘yancin gashin kai, kasancewa ƙananan hukumomin sun fi kusanci ga jama’a, masanan na ganin hakan zai taimaka wajen samar da ayyukan ci gaba a matakin farko.