Ana neman mutum takwas da ake zargi da kisan sojin Najeriya 17

Spread the love

Hedikwatar tsaron Najeriya ta ce tana neman wasu mutum takwas ruwa a jallo saboda zargin su da hannu a kisan sojoji 17 a yankin Okuama da ke jihar Delta.

Daraktan yaɗa labaran tsaro Manjo Janar Edward Buba ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da aka yi a hedikwatar tsaron da ke Abuja, babban birnin Najeriya.

Hedikwatar tsaron ta fitar da sunayen mutanen takwas ranar Alhamis da suka haɗa da farfesa Ekpekpo Arthur da Andaowei Dennis Bakriri da Akevwru Daniel Omotegbo sai Akata Malawa David da Sinclear Oliki da Clement Ikolo Ogenerukeywe da Reuben Baru sai kuma Igoli Ebi.

Buba ya yi kira ga masu ruwa da tsaki da sarakunan gargajiya a faɗin Najeriya musamman a yankin Neja Delta su taimaka wa sojoji wajen zaƙulo waɗanda aka ayyana ana neman ruwa a jallo.

A ranar 14 ga watan Maris ne wasu ɓata-gari suka afka wa sojojin da ke aikin wanzar da zaman lafiya tsakanin al’umomin yankunan Okuoma da Okoloba inda suka kashe su.

A ranar Laraba ne kuma aka yi jana’izar sojojin a maƙabartar sojoji ta ƙasa da ke Abuja inda shugaba Bola Tinubu ya halarta tare da wasu manyan jami’an gwamnati.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *