Ana neman wata sarauniyar kyau a Najeriya kan zargin safarar kwaya

Spread the love

Hukumomi a Najeriya sun bayyana wata sarauniyar kyau a shekarar 2015 a matsayin wadda ake nema ruwa a jallo saboda zarginta da hannu a safarar miyagun kwayoyi.

Har Yanzu Kuna Tare Da Mu —Martanin ECOWAS Ga Nijar, Mali Da B/Faso

Burkina Faso da Mali da Nijar sun fice daga ECOWAS

Bayanai na cewa Aderinoye Queen Christmas da aka fi sani da Sarauniya Oluwadamilola Aderinoye ta tsere wa jami’ai daga hukumar yaƙi da sha da fataucin haramtattun ƙwayoyi, NDLEA a lokacin da suka kai samame gidanta da ke Legas a makon da ya gabata.

Cikin wata sanarwa, hukumar ta ce an kai samamen ne bayan wasu sahihan bayanai da suka nuna cewa tsohuwar sarauniyar kyan tana da hannu a ta’amali da haramtattun kwayoyi.

“Abubuwan da aka gano a gidanta bayan binciken da jami’ai suka yi akwai gram 606 na kwayar Canadian Loud sai tabar wiwi da abin gwada nauyi da manya-manyan ma’ajin magunguna na roba,” kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Wadda ake zargin ta taba lashe gasar kyau ta Miss Commonwealth Nigeria Culture a shekarar 2015/2016 kuma ita ce ta kafa gidauniyar Queen Christmas.

Kawo yanzu dai ba ta ce komai ba game da zargin da ake mata.

Ko a benci Ahmed Musa na mana amfani – Peseiro

Shi ma wani da ake zargi, da ya dawo daga Brazil a makon da ya gabata, an cafke shi a filin jirgin sama na Murtala Muhammed saboda hadiye manyan kullin tabar wiwi 60, kamar yadda hukumar ta NDLEA ta bayyana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *