Kungiyar agaji ta likitoci watau MSF ta nuna damuwa kan yadda ake ci gaba da samun ƙaruwa a yawan yara da ke fama fa lalurar tamowa ko rashin abinci mai gina jiki a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya.
Ta ce matsalar tafi kamari a yankunan Shinkafi da Zurmi inda ta yi wa yara fiye da dubu 97 gwaji kuma sakamakon ya nuna cewa kashi 27 cikin 100 daga cikinsu na fama da tamowa.
Gwaje-gwajen da aka yi a watan Yuni da ya gabata a yankunan ya nuna cewa fiye da kashi 20 cikin ɗari na yaran da aka yi wa gwajin na fama da rashin abinci mai gina jiki a matakin farko watau lalurar ba ta yi tsanani a jikinsu ba.
Sai dai ƙungiyar ta nuna damuwa kan rashin maganin da ke ɗauke da sinadarin abinci mai gina jiki da ake amfani da shi wajen magancewa yaran matsalar sakamakon dakatar da aikin samar da abinci da asusun kula da yara na UNICEF ya yi a farkon shekarar da mu ke ciki.
MSF ta ce rashin wannan magani mai ɗauke da sinadaran ƙarin kuzari da ake ba wa yaran masu lalurar ta tamowa a yankin arewa maso yammacin Najeriyar zai iya saka rayuwar yaran cikin haɗari tare da tsananta lalurar a jikinsu in ba a yi gaggawar ɗaukar mataki ba.
Ta jaddada buƙatar ganin cewa an ɗauki ƙarin matakan shawo kan matsalar saboda a cewarta matsalar ta riga ta kai kololuwa kuma rashin maganin ya sa ana cigaba da samun ƙaruwa a yawan yara masu fama da wannan lalura.
MSF ta ce ma’aikatanta sun yi wa yara fiye da dubu bakwai magani tun daga watan Janairun zuwa watan Yulin bana a yankunan Shinkafi da da Zurmi da Gummi da kuma Talata Mafara.
Kuma a cewarta adadin yaran da aka kwantar a daidai wannan lokaci a shekarar 2023 ya zarce da kashi talatin da biyar cikin ɗari.
“Mun kuma lura da yadda ake cigaba da samun ƙaruwar yara da ke kamuwa da wasu cututtuka da ake iya magancewa da allurar rigakafi ciki har da ƙyanda da malariya da amai da gudawa, a shekarar nan kaɗai mun warkar da yara masu fama da kyanda kusan 5,700,” in ji MSF.